logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu ci gaba wajen inganta hidimomin renon yara kanana

2024-02-29 11:22:49 CMG Hausa

Hukumar kula da lafiya ta Kasar Sin, ta ce kasar ta kara matsa kaimi wajen bunkasa hidimomin renon yara ‘yan kasa da shekaru 3, cikin aminci.

Yang Jinrui, babban jami’i a hukumar, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, a yanzu kasar Sin na da gidajen renon yara ‘yan kasa da shekaru 3, kimanin guda dubu 100, wadanda ke iya daukar yara miliyan 4.8.

Ya kara da cewa, a kokarinta na ragewa iyaye dawainiya, a baya-bayan nan kasar Sin ta kara samarwa karin iyalai hidimomin renon yara. (Fa’iza Mustapha)