logo

HAUSA

“Qiu Shi” za ta wallafa sharhi mai taken “Kara kyautata ayyukan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa”

2024-02-29 19:57:48 CGTN HAUSA

Mujallar “Qiu Shi”, za ta wallafa wani sharhi mai taken “Kara kyautata ayyukan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa don raya demokuradiyya a dukkan fannoni ta hanyar yin shawarwari” a ran 1 ga wata mai zuwa.

An hada wannan sharhi ne bisa wasu bayanai dake cikin jawaban shugaban kasar Sin Xi Jinping, na tsakanin watan Fabrairun shekarar 2013 zuwa watan Yunin shekarar 2023. (Amina Xu)