logo

HAUSA

GDPn Kasar Sin Na Shekarar 2023 Ya Karu Da Kashi 5.2 Cikin Dari

2024-02-29 14:51:58 CMG Hausa

Yau Alhamis, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da “sanarwar alkaluman tattalin arzikin al’umma da bunkasuwar zamantakewa ta shekarar 2023 ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin”.

Alkaluman sun bayyana cewa, yawan GDPn kasar na shekarar 2023 ya kai triliyan 126.0582, wanda ya karu da kashi 5.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2022, kuma yawan GDP ga kowane mutum ya kai dubu 89.358, wanda ya karu da kashi 5.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2022. Yawan kudin shiga na jama’ar kasar ya karu da kashi 5.6 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2022. Ingancin gudanar da aiki na jama’a ya karu da kashi 5.7 cikin dari bisa makamancin lokaci na 2022. (Safiyah Ma)