Wakilin kasar Sin ya yi kira da a dauki matakai don dakile tasirin da rikicin Gaza ke yi a Syria
2024-02-28 11:35:55 CMG Hausa
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, a ranar Talata ya yi kira da a dauki matakai don dakile illar da rikicin Gaza ya haifar a kasar Syria.
Dai Bing ya shaidawa taron kwamitin sulhu game da Syria cewa ,"A cikin watanni 4 da suka gabata, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama a wurare daban-daban na kasar Syria ta tuddan Golan da ta mamaye, wanda kasar Sin ta damu matuka, muna kira ga dukkan bangarorin da su yi taka-tsantsan, kar rikicin ya kara tsananta,"
Wakilin ya kara da cewa, "kasashen da ke wajen yankin ya kamata su taka rawar gani wajen ganin an daidaita al'amura tare da hana rikicin fadada."
Dai ya bukaci kasashen duniya da su kiyaye ka'idar Syria, da karfafa tattaunawa da tuntubar juna, da samar da mafita mai karbuwa ga dukkan bangarorin. "Mun yi imanin cewa taimako daga kasashen yankin zai samar da wani sabon tsari na daidaita batun Syria a siyasance," a cewar Dai. (Yahaya)