logo

HAUSA

Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba barazana ba, dama ce ga duniya

2024-02-28 08:15:17 CMG Hausa

Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya samo asali ne sakamakon matakan da kasar ta dauka na daidaita fannonin tattalin arzikinta. A cikin shekaru fiye da 45 da suka gabata, kasar Sin ta aiwatar da matakan bude kofa ga waje da dama, da rage tsauraran matakan shigowa cikin kasar, da inganta yanayin da ya dace ga kamfanonin waje don zuba jari a kasar. Yadda kasar Sin ke kara ci gaba, haka take kara bude kofarta, ta kasance abin dogaro ga masu zuba jari a duniya. Aiwatar da dokar zuba jari ga kasashen ketare da daidaita ka'idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa sun kara inganta tsarin zuba jarin waje, Amma duk da haka, kasashen Yamma na kallon ci gaban tattalin arzikin Sin a matsayin barazana a maimakon dama ga ci gaban duniya, Shin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin dama ce ga duniya ko barazana? Lallai ci gaban tattalin arzikin Sin dama ce ga duniya ba barazana ba. 

Bisa binciken da CGTN da jami'ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar ta cibiyar binciken sadarwar kasa da kasa ta New Era, sama da kashi 90 cikin 100 na wadanda aka yiwa tambaya a duniya sun bada amsar cewa, kasar Sin kasa ce mai muhimmanci, kuma zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da kasar Sin na nufin moriyar kansu. Kuma suka ce hakan ta wata zama yarjejeniya ta gama gari a tsakanin kasashen duniya.

Fiye da kashi 80 cikin 100 na kamfanonin ketare sun gamsu da yanayin tattalin arzikin kasar Sin a bara, yayin da sama da kashi 90 cikin 100 suka yi imanin cewa, kasuwar kasar Sin na da armashi, a cewar wani rahoto kan sakamakon binciken da majalisar bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin ta wallafa.  

Idan aka yi la'akari da tarihi, bunkasuwar kasar Sin wani babban dalili ne na ci gaban dukkan bil'adama. Kasar Sin ta yau ba ta Sinawa kadai ba ce, ta zama kasar Sin ta duniya baki daya. Yayin da adadin ci gaban kasar Sin ya karu da kashi daya cikin dari, ci gaban sauran kasashe ya karu da kashi 0.3 cikin dari, bisa ga binciken IMF. Kasar Sin na ci gaba da himmatuwa wajen inganta yanayin kasuwanci da tattalin arzikinta ga masu zuba jari, kuma tana kara kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya. (Muhammed Yahaya, Saminu Alhassan, Sanusi Chen)