logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Nijar ya gana da shugaban tawagar tarayyar Turai da jakadun kasashe mambobin kungiyar EU

2024-02-28 09:50:51 CMG Hausa

 

Ministan harkokin waje, da dangantaka da kuma ’yan Nijar dake ketare, Bakary Yaou Sangare ya tattauna a ranar jiya Talata 27 ga watan Fabrairun shekarar 2024 a fadar faraminista dake birnin Yamai, tare da shugaban tawagar tarayyar Turai dake kasar Nijar da jakadun kasashe mambobin kungiyar dake da wakilci a jamhuriyar Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Bisa tsohon salon tattaunawar siyasa tsakanin kasar Nijar da tarayyar Turai ne, wannan musanya tsakanin ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare da wakilan kungiyar tarayyar Turai a karkashin jagorancin shugaban tawagar, mista Salvador Franca Da Silva ta maida hankali kan dangantakar dake tsakanin Nijar da kungiyar EU, da kuma abubuwan baya bayan nan da suka shafi ci gaban huldar bangarorin biyu.

Tattaunawar yarda da mutunta juna sun gudana domin karfafa dangantaka da tabbatar da alkawuran da aka daukar ma juna.

Haka kuma, wannan ganawa ta taimaka wajen samun damar yin musanyar bayanai, da bada kwarin gwiwa domin fahimtar juna da saukaka tantance muhimman maradu da sharudan ci gaba na moriyar juna.

Nijar da abokan huldarta, mu tunatar muke da cewa, bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, wasu kasashe abokan huldar Nijar sun dakatar da dangantakarsu. Sabbin hukumomin Nijar a karkashin jagorancin shugaban majalisar ceton kasa ta CNSP, birgadiye janar Abdourahamane Tiani sun sake duba taswira wannan siyasa ta dangantaka tare da aza wata sabuwar alkibla.

Dalilin haka ne, wannan tattaunawa tsakanin Nijar da abokan huldarta, yawancinsu suka bayyana fatansu na ci gaba da dangantakarsu bisa sabbin manufofi masu tushe dake dogaro da girmama moriyar kasar Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.