An kaddamar da littafi a kan ka’idodjin da kamfanonin kasashen waje za su rinka bi wajen baiwa ’yan kasa aiki a Najeriya
2024-02-28 09:48:46 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da littafi da zai jagoranci kamfanoni mallakin ’yan kasashen ketare dake Najeriya wajen sanin ka’idojin da za su rinka bi idan sun tashi daukar ’yan kasa aiki, littafin kuma yana kunshe da sabon tsarin harajin ci gaban kasa da kamfanonin za su rinka biyan gwamnati.
Da yake jawabi yayin bikin a fadarsa dake birnin Abuja, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, wannan tsari da aka bullo da shi ba zai taba haifar da wata matsala ba ga ’yan kasashen waje masu sha’awar zuba jari a Najeriya.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Haka kuma shugaban na tarayyar Najeriya ya ce, wannan munufa an kirkiro ita ne domin sanya ido kan ma’aikata baki ’yan kasashen waje tare kuma da tilastawa mamallaka kamfanonin biyan haraji ga kowanne daya daga cikin ma’aikatan da suka dauko daga waje domin ya yi msu aiki.
Haka zalika wannan sabon tsari zai bayar da damar habaka kwazon ma’aikata ’yan kasa tare kuma da rage dogaro da ma’aikata baki, duk dai domin tabbatar da ganin irin wadannan kamfanoni sun fi nuna fifiko ga ’yan Najeriya ta fuskar daukar aiki.
Baya ga kara karfafa tsarin samar da kudaden shiga ga kasa da kuma lura da zirga-zirgar baki, haka kuma Shirin “yana da karfin da zai iya toshe duk wasu matsaloli da suka yi wa kasar nan tarnaki wajen tunkarar kalubalen tsaro.”
A jawabinsa, ministan harkokin cikin gida na tarayyar Najeriya Mr Olubunmi Tunji-Ojo ya jaddada cewa, “Babban makasudin shirin dai shi ne a tabbatar da ganin cewa duk ma’aikacin da kamfanonin za su shigo da shi kasar nan domin aiki, sai lallai cewa babu dan Najeriyar da yake da kwarewa ta yin wannan aiki.” (Garba Abdullahi Bagwai)