logo

HAUSA

Kasar Sin ta fadada tsarin sufuri don tabbatar da ci gaba mai inganci

2024-02-28 13:57:59 CMG Hausa

Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta sanar a ranar Laraba cewa, kasar Sin ta samu gagarumar nasara wajen inganta tsarin sufuri a shekarar da ta gabata.

Li Xiaopeng, ministan sufuri ya shaidawa taron manema labarai cewa, jarin da aka zuba a kadarorin tsarin sufurin kasar ya kai yuan triliyan 3.9 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 548.7 a shekarar 2023.

Li ya kara da cewa, an kaddamar da layukan dogo na jiragen kasa masu saurin tafiya da tsawonsu ya kai kilomita 2,776, kuma an gina ko fadada hanyoyin mota na tsawon kilomita 7,000 a bara.

Kasar ta kara ko inganta hanyoyin sufuri na jiragen ruwa na tsawon kilomita 1,000, kuma adadin filayen jiragen sama na sufuri ya kai 259. Ana ba da hidimomi na gidan waya ga duk kananan hukumomin kasar. (Yahaya)