Wakilin Sin ya yi kira ga bangarori daban daban su inganta harkokin takaita yaduwar makamai da kwance damarar soja na kasa da kasa
2024-02-28 13:50:09 CMG Hausa
Shugaban hukumar kula da takaita yaduwar makamai na ma’aikatar harkokin wajen Sin, Sun Xiaobo ya gabatar da jawabi a babban taron tattaunawa kan kwance damarar soja na Geneva da ake gudanarwa mako-mako, inda ya yi kira ga bangarori daban daban su tsaya tsayin daka kan ra’ayin makomar bai daya ta daukacin bil’adama, da kuma inganta harkokin takaita yaduwar makamai da kwance damarar soja na kasa da kasa.
Sun Xiaobo ya bayana cewa, ana fuskantar yanayin tsaro mai tsanani a kasa da kasa, don haka ya kamata taron tattaunawar ya ba da gudummawarsa. Da farko, ya kamata a bi ra’ayin bangarori daban daban, kuma a cimma tsaro cikin hadin gwiwa. Na biyu shi ne, kiyaye matsayar da aka cimma na rage makaman nukiliya da inganta gudanar da harkokin rage makaman nukiliya. Na uku shi ne mai da hankali kan bunkasuwa da tsaro da nuna adawa da neman raba-gari da sauran kasashe. Nu hudu shi ne dora muhimmanci kan tsara ka’idojin kasa da kasa da tinkarar kalubalolin fasahohin zamani kamar fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama, da sararin samaniya da yanar gizo da sauransu. Daga karshe dai shi ne inganta gudanar da yarjejeniya a fannin ilmin halittu da halayyar albarkatun kasa, da kiyaye mutuncin tsarin yarjejeniyar takaita yaduwar makamai.
Sun Xiaobo ya kara da cewa, gine-ginen tsaron kasa da ci gaban kasar Sin a ko da yaushe na da nufin biyan halaltattun bukatun tsaronta, kuma ya kasance karfin ci gaban dakarun zaman lafiya na duniya. (Safiyah Ma)