logo

HAUSA

Yaushe za a tabbatar da tsagaita bude wuta a zirin Gaza?

2024-02-28 21:43:37 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Kwanan baya, Amurka ta sake jefa kuri’ar nuna rashin amincewa da wani daftarin kudurin da kasar Aljeriya ta gabatar dangane da batun Gaza a kwamitin sulhu na MDD, karo na hudu ke nan da ta jefa kuri’ar rashin amincewa da daftarin kuduri game da batun tsagaita bude wuta a Gaza, tun bayan barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila a watan Oktoban bara.

Hakan ya sa kasashe da dama ciki har da kasar Sin fusata, inda suke ganin cewa, “matakin ya nuna amincewa da kisan kiyashi da ake yi” “Kwamitin sulhu ya shaida wani mummunan babi na daban da Amurka ta rubuta”.

Tun bayan barkewar rikicin, Palasdinawa kusan dubu 30 sun halaka a matakan soja da Isra’ila ta dauka a zirin Gaza, baya ga wasu sama da dubu 70 da suka ji raunuka. Amma me ya sa Amurka ta yi shiru a kan batun tsagaita bude wuta, har ma ta yi kokarin kawo cikas ga kokarin da sauran kasashe suka yi?

A hakika, huldar dake tsakaninta da Isra’ila na da muhimmiyar ma’ana gare ta. Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya taba bayyanawa a jawabin da ya gabatar a shekarun da suka gabata cewa, “Da a ce babu Isra’ila, to Amurka za ta kirkiro Isra’ila don kare muradunta a yankin gabas ta tsakiya.” Kasancewar Isra’ila kasa ce mai karfi ta fannin soja da leken asiri, Amurka na daukarta a matsayin babban makaminta a yankin gabas ta tsakiya, abin da ya sa Amurka ta dade tana nuna goyon baya ga Isra’ila. A sa’i daya kuma, daidai kamar yadda ta yi a yakin Afghanistan da rikici a tsakanin Rasha da Ukraine, masana’antun samar da makaman soja na Amurka da sauran masu ruwa da tsaki sun ci kazamar riba sakamakon rikicin da ya barke.

Amurka tana cin gajiya idan ta nuna goyon baya ga Isra’ila, kuma a gaban tarin riba, abin da a bakinta na wai “dimokuradiyya da hakkin dan Adam” ba kome ba ne.

Yanzu haka sabon zagayen shawarwari kan batun tsagaita bude wuta a zirin Gaza na gudana a kasar Qatar. Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana a jiya 26 ga wata cewa, an kusan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin Isra’ila da Hamas, kuma ya yi fatan ganin sassan biyu za su cimma tsagaita bude wuta kafin Litinin mai zuwa.

Da fatan shugaba Biden ya fadi gaskiya, da fatan kuma da gaske ne Amurka na sulhuntawa yadda ya kamata a wannan karo. Muna fatan ganin an tabbatar wa al’ummar zirin Gaza da zaman lafiya a dab da zuwan watan Ramadan mai tsarki. (Mai Zane: Mustapha Bulama)