Kasar Sin za ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin gina budadden tsarin tattalin arziki na duniya
2024-02-27 13:58:12 CMG Hausa
A jiya Litinin ne aka bude taron kwanaki hudu na ministoci karo na 13 na hukumar cinikayya ta duniya (WTO) a ABU DHABI, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa wanda ya samu halarcin ministocin tattalin arziki, cinikayya da raya kasa daga kasashe daban-daban, da wakilai daga kungiyoyin tattalin arziki da cinikayya na duniya.
Wang Wentao, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, WTO muhimmin ginshiki ne na bangarori daban-daban, kuma wani muhimmin mataki na tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya.
Wang ya ce, gwamnatin kasar Sin tana kare tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kuma tana mai da hankali sosai kan ayyukan hukumar WTO, inda ya kara da cewa, kasar Sin za ta yi aiki tare da dukkan bangarori don gina budadden tsarin tattalin arzikin duniya.
Taron ministocin shi ne kwamitin yanke shawara mafi girma na kungiyar WTO, wanda ke da alhakin ciyar da shawarwari kan muhimman batutuwa gaba, da yin nazari kan ayyukan yau da kullum na WTO, da tsara alkiblar ci gaba na tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban. (Muhammed Yahaya)