Wang Yi: Kasar Sin za ta ba da sabbin gudummawa don bunkasa harkokin kare hakkin dan Adam na duniya
2024-02-27 13:58:04 CMG Hausa
A jiya Litinin ne kasar Sin ta lashi takobin yin hadin gwiwa tare da dukkan bangarori wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga bil’Adama, da kuma ba da sabbin gudummawa ga bunkasuwar harkokin kare hakkin dan Adam na duniya, yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a taron majalisar kare hakkin dan Adam karo na 55.
Wang ya ce, “muna adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe da kuma dakile ci gabansu da sunan kare hakkin dan Adam. Ya kuma jaddada wajabcin mutunta zabin kasashe kan turbar raya hakkin dan Adama. Ya kara da cewa, “ya kamata mu dage kan hadin gwiwar samun nasara tare da ba da shawarwari wajen cimma matsaya.”
Da yake tabo batun rikicin Hamas da Isra'ila, Wang ya ce, "Kare hakkin dan Adam na kowace kabila da kowane mutum bisa gaskiya, da daidaito kuma ta hanya mafi dacewa nauyi ne da ya rataya a wuyan kasashen duniya." (Muhammed Yahaya)