logo

HAUSA

An fara aiki da cibiyar watsa labaran “manyan taruka biyu” na 2024 na kasar Sin

2024-02-27 13:49:41 CMG Hausa

A yau Talata ne aka fara aiki da cibiyar watsa labaran “manyan taruka biyu” na 2024 na kasar Sin, wato taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar, da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar.

An ce, kawo yanzu, sama da ‘yan jarida 3000 na gida da waje, sun yi rajistar ba da rahotannin tarukan biyu, wadanda suka hada da ‘yan jaridan gida sama da 2000, da kuma sama da 1000 da suka zo daga ketare, adadin da ya karu sosai idan an kwatanta da na shekarun baya. (Lubabatu)