logo

HAUSA

Takunkumai Kan Kamfanonin Sin Ba Su Ne Maganin Rikicin Ukraine Ba

2024-02-27 16:39:50 CGTN HAUSA

DAGA Fa’iza Mustapha

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana matukar adawa da haramtattun takunkumai daga bangare guda da Amurka ta kakkabawa kamfanonin kasar. Haka kuma ta bayyana cewa, kasar za ta dauki matakan da suka wajaba, don kare halastattun hakkokinta, da moriyar kamfanoninta yadda ya kamata.

Abu ne da ya zama wajibi, kowace kasa mai cikakken iko, kuma wadda ta san ciwon kanta, ta tabbatar da kare moriyarta da na al’ummomi da dukkan wani abu mallakinta. Haka kuma, dole ne a rika tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, wato kamar yadda Sin ta bayyana cewa za ta dauki matakan da suka wajaba na kare muradunta.

Sai dai, bisa wani yanayi mara dadi da daukacin duniya ke ciki, da kira da burin da kasashen duniya ke da shi na ganin kyautatuwar mu’amala tsakanin manyan kasashen biyu, wato Sin da Amurka, kiran da ake yi har kullum shi ne, a kai zuciya nesa, a girmama tare inganta tattaunawa da juna.  Bai kamata Amurka ta rika takala har ta kai Sin ga mayar da martani ba.

Dakile alaka ko kamfanonin Sin ko kuma katse huldar Sin da Rasha, ba shi ne zai kawo karshen rikicin Ukraine ba. Sin mai kaunar zaman lafiya, ta sha bayar da shawarwarin yadda za a shawo kan rikicin, haka kuma tana ci gaba da yin iyakar kokarin ganin an tsagaita bude wuta, sai dai da alama, tamkar ana tufka ne da warwara, domin yayin da take neman shawo kan rikicin, har yanzu wasu kasashen yamma na ta matsa kaimi wajen goyon bayan wani bangare tare da tallafa masa, lamarin da kowa ya san cewa, ba hanya ce ta samar da maslaha ba.

Zuwa yanzu bisa la’akari da halin da duniya ta shiga, ya kamata mu gane cewa, takunkumai ko fito na fito ko karfin soji, ba za su kawo karshen rikicin ba, ganin yadda aka shafe shekaru 2 ana gwabza fada amma babu alamar tsagaituwarta. Yanzu lokaci ne da ya kamata a sauya dabara, domin lalubo mafita mai dorewa ga rikicin, ba tare da sanya siyasa ko bata alaka ko dora laifi kan wata kasa ba. (Fa’iza Mustapha)