logo

HAUSA

Adadin kamfanonin waje dake zuba jari a Sin na karuwa

2024-02-27 19:30:35 CMG Hausa

A watan Janairun bana, kasashe masu ci gaba na yammacin duniya sun kara yawan jarin da suke zubawa a kasar Sin. A cikin su, Faransa ta kara yawan jarin ta da ninki 25, yayin da Sweden ta kara na ta da ninki 11, kana Jamus ta kara da kaso 211.8, yayin da Australia ta kara na ta jarin da kaso 186.1%.

Ta ayyukan su na zahiri, wadannan kasashe sun yi watsi da kalaman kafofin yamma dake cewa wai "Kamfanonin dake zuba jarin waje a kasar Sin” na ficewa daga kasar.

A idanun kamfanoni masu jarin waje, fifikon Sin a hada hadar sarrafa hajoji, da babbar kasuwar kasar, da fannin tattalin arziki na dijital dake bunkasa, da ma damammakin dake akwai a fannin ci gaba mai dorewa, dukkanin su karfi ne dake ingiza cimma nasarorin su.

Wani rahoton bincike mai nasaba da hakan ya yi nuni da cewa, sakamakon gabatar da manufofin bunkasa zuba jari a Sin, fadi da kuma girman jarin waje da Sin ke jawowa zai ci gaba da bunkasa a nan gaba.   (Saminu Alhassan)