logo

HAUSA

Rana Ba Ta Karya: Habakar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Ba Mahassada Kunya

2024-02-27 16:39:10 CGTN HAUSA

 

Idan muka kalli halin da duniya ke ciki a natse, za mu ga cewa, illolin da ke tattare da tsauraran manufofin kudi na manyan tattalin arziki sun yi fice.  Hadarin dake tattare da rashin hadin kai, babakare, rikice-rikice na yanki da siyasar kasa da kasa suna karuwa, kuma tattalin arzikin duniya yana kara tabarbarewa. Amma duk da wannan barazanar, tattalin arzikin Sin na nan da karfinsa daram.

Kar a yaudare ku da labarun karya, Jimillar GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.2 cikin dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 126.06 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 17.71 a shekarar 2023, bisa ga bayanan da hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar.  Sin ta ba da gudummawar sama da kashi 30 cikin 100 ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya tsawon shekaru a jere, tana matsayin gaba a cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya kuma a  matsayin babbar injin ci gaban tattalin arzikin duniya.

Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya samo asali ne sakamakon matakan da kasar ta dauka na daidaita fannonin tattalin arzikinta. A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta aiwatar da matakan bude kofa ga waje da dama, da rage tsauraran matakan shigowa cikin kasar, da inganta yanayin da ya dace ga kamfanonin waje don zuba jari a kasar. Yadda kasar Sin ke kara ci gaba, haka take kara bude kofarta, ta kasance abin dogaro ga masu zuba jari a duniya. Aiwatar da dokar zuba jari ga kasashen ketare da daidaita ka'idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa sun kara inganta tsarin zuba jarin waje.

Fiye da kashi 80 cikin 100 na kamfanonin ketare sun gamsu da yanayin kasuwancin kasar Sin a bara, yayin da sama da kashi 90 cikin 100 suka yi imanin cewa, kasuwar kasar Sin na da armashi, a cewar wani rahoto kan sakamakon binciken da majalisar bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin ta wallafa.  

Idan aka yi la'akari da tarihi, bunkasuwar kasar Sin wani babban dalili ne na ci gaban dukkan bil'adama. Kasar Sin ta yau ba ta Sinawa kadai ba ce, ta zama kasar Sin ta duniya baki daya.  Yayin da adadin ci gaban kasar Sin ya karu da kashi daya cikin dari, ci gaban sauran kasashe ya karu da kashi 0.3 cikin dari, bisa ga binciken IMF. Kasar Sin na ci gaba da  himmatuwa wajen inganta yanayin kasuwanci ga masu zuba jari, tana kara kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya, yayin da mahassada ke jiran labarin rugujewar tattalin arzikinta. (Muhammed Yahaya)