logo

HAUSA

Yankin Dosso ya karbi bakuncin wata haduwar al’adun kan iyaka bisa taken hadin kan al’umma da zaman lafiya

2024-02-27 09:57:40 CMG Hausa

A yankin Dosso, a karamar hukumar karkarar Dankatsari dake cikin gundumar Dogondoutchi, an gudanar da bikin al’adu na kan iyaka a ranakun 24 zuwa 26 ga watan Fabrairun shekarar 2024. Maudu’in bikin shi ne bunkasa zaman lafiya, tsaro da kuma hadin kan al’umma a yankunan dake kusa kan iyakokin kasashe.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A tsawon wadannan kwanaki uku, an gabatar da wasanni da dama na al’adu da motsa jiki da suka hada da kokowar gargajiya, tseren gudu da kuma raye-raye na gargajiya. Mutanen yankunan Nijar guda takwas dake wakiltar kabilun kasar suka amsa kiran wannan babban bikin al’adun kan iyaka, har ma da na sauran kasashe makwabta kasar Nijeriya da Benin.

Bando Kaka, magajin garin Dankatsari ya yi mini karin haske kan wannan bikin wasannin al’adu na kan iyaka da kuma muhimmancinsa a daidai wannan lokaci da Nijar take bukatar dunkulewar al’ummarta.

“Kasarmu tana da kabiloli iri iri da suke zaune wuri guda, ke nan kabilolin idan ana son su ji dadin zama tare, tun da tun dama ana zaman tare, kuma ana auren juna ke nan abin ya ci gaba, me ya kamata a yi, al’adunmu da muka san na da ne su ne ya kamata mu farfado, mu kara zumunci tsakaninmu, shi ne mu muke son mu farfado da su idan Allah ya yarda, don al’ummarmu su ji dadin zama da juna. Tun da duk inda aka game aka yi wasa, kowane ya ga wasan wani, sai ka iske wani na rawar wata kabila, sai ka ga buzu na rawar goge, sai ka ga ba’are na rawar tande, ko bagube na rawar tande, ka ga abin yana da amfani. Ke nan shi ne muke son mu ci gaba da shi idan Allah ya yarda, shekara duk mu shirya wannan biki. Burinmu mu samu hadin kan al’ummarmu, a samu kwanciyar hankali a cikin kwamin din mu, a cikin jiharmu, a cikin kasarmu gaba daya, shi ne babban burinmu. Tun da muna tsammanin duk idan ana wasa ko da yaushe ana gaggamewa, insha Allahu za’a samu hadin kai, za’a samu kwanciyar hankali.”

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.