logo

HAUSA

Shugaban Palasdinu ya amince da murabus din gwamnatin kasar mai ci

2024-02-27 13:48:58 CMG Hausa

Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Palasdinu ya bayar, an ce, a jiya Litinin 26 ga watan nan, shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas, ya amince da bukatar murabus din da firaminista Mohammad Shtayyeh ya gabatar masa, sai dai ya bukaci gwamnatin da firaministan ke jagoranta, da ta ci gaba da gudanar da aikinta, har zuwa lokacin kafuwar sabuwar gwamnati.

A gun wani taron ayyukan gwamnati da aka gudanar da safiyar jiyan, Mohammad Shtayyeh ya sanar da murabus din gwamnatin da yake jagoranta, inda ya ce, matakin na da alaka da hare-haren da al’ummar zirin Gaza ke fuskanta, da ma sauran matsalolin da hakan ya haifar ta fannonin siyasa, da tsaro da tattalin arziki, da kuma tabarbarewar yanayin tsaro a yankunan Kudus, da ma yammacin gabar kogin Jordan. (Lubabatu)