logo

HAUSA

Sin ta yi alkawarin kara janyo jarin waje

2024-02-27 13:44:42 CMG Hausa

 

Masu karatu, barka da war haka. Kwanan baya, a taron majalisar gudanarwa da firaministan kasar Sin Li Qiang ya jagoranta, da taron aikin jarin waje na shekarar 2024 da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta kira, an sanar da cewa, a bana, kasar Sin za ta kara karfin janyo hankulan masu zuba jari na kasashen waje.