logo

HAUSA

Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci jana'izar marigayi shugaba kasar Namibia Hage Geingob

2024-02-26 15:51:56 CMG Hausa

Tun daga ranar 24 zuwa 25 ga wannan wata, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), Jiang Zuojun ya halarci jana'izar marigayi shugaban kasar Namibia Hage Geingob da aka gudanar a birnin Windhoek. A ranar 25 ga wata da yamma, sabon shugaban kasar Nangolo Mbumba ya gana da manzon musamman Jiang Zuojun a fadar shugaban kasar.

Jiang Zuojun ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Mbumba, tare da mika ta’aziyya ga rasuwar marigayi shugaba Hage Geingob, da kuma jajantawa gwamnatin kasar Namibia da jama’arta.

A nasa bangare, shugaba Mbumba ya nuna godiyarsa ga shugaba Xi Jinping da ya tura manzon musamman zuwa kasar, kana ya jaddada cewa, kasarsa ta Namibia za ta ci gaba da yin kokari tare da kasar Sin don kara sada zumunta a tsakaninsu da amfanawa kasashen biyu da jama’arsu. (Zainab Zhang)