logo

HAUSA

Hukumar EFCC za ta binciki laifukan kudi 3,000

2024-02-26 13:23:20 CMG Hausa

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati wato EFCC a jiya Lahadi ta bayyana shirinta na gudanar da bincike kan wasu laifuka 3,000 da suka shafi laifukan kudi a fadin kasar domin dakile rashin gaskiya.

A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya samu a ranar Lahadin da ta gabata, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC, Ola Olukoyede, ya ce kararraki 3,000 da aka amince a gudanar da bincike a kansu na daga cikin kararraki sama da 5,000 da EFCC ta samu.

Olukoyede ya bayyana cewa, laifukan da aka yi wa rajista don gudanar da bincike sun shafi dimbin laifuffukan kudi, da suka hada da zamba, almundahanar kudi, satar kudi a wurin aiki, da laifukan yanar gizo. (Yahaya)