logo

HAUSA

Masanin kasar Zambia: Tattalin arzikin Sin ginshike ne ga duniya

2024-02-26 11:11:01 CMG Hausa

Masanin tattalin arziki na kasar Zambia, Kelvin Chisanga, ya bayyana tattalin arzikin kasar Sin a matsayin mai kuzari, inda ya kara da cewa, duniya za ta amfana da shawarwari da kasar ta gabatar.

Masanin wanda ke zaune a birnin Lusaka ya ce tsarin tattalin arzikin kasar Sin ya sa kasar ta zama mai juriya, duk da kafafen yada labarai na kasashen yamma na yayata akasin hakan. 

Ya kara da cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya kasance mai kuzari, kuma yadda kasar ke tafiyar da tattalin arzikinta, abun burgewa ne. 

A cewarsa, Sin ta gina tubali mai karfa na kirkiro dabaru da raya masana’antu da yin hadin gwiwa mai karfi. Yana mai cewa, ta zama jigo ga kasuwar duniya. 

Bugui da kari, ya ce a shirye Zambia da sauran kasashen Afrika suke su zurfafa hadin gwiwa da Sin domin cimma moriyar juna daga tattalin arzikinta mai karfi. Yana mai cewa, ya kamata kasashen Afrika su tabbatar da sun gano hanyoyin hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban-daban. (Fa’iza Mustapha)