Sabon shirin kasar Sin zai taimakawa raya masana'antu a Afirka
2024-02-26 15:11:01 CMG Hausa
A wajen wani taron da shugabannin kasar Sin suka kira a kwanan baya, dangane da aikin raya tattalin arziki, an jaddada muhimmancin manufar raya sabon karfin samar da bunkasuwa. Makasudin wannan manufa shi ne sa kaimi ga kokarin kirkiro sabbin fasahohi, daga baya a yi amfani da fasahohin da aka samar wajen raya masana'antu. Kana manufar ta kunshi fannonin da suka hada da inganta tsoffin masana'antu ta hanyar fasahar zamani, da raya sabon makamashi, da harkar sadarwa, da sauran sabbin ayyukan masana'antu. Gami da raya masana'antun da za su samar da amfani a nan gaba, kamar masu alaka da na'ura mai kwakwalwa ta kwamfuta irin na Quantum, da fasahar sadarwa ta 6G, da dai sauransu, da kuma horar da kwararrun ma'aikata da za su iya sarrafa sabbin fasahohi.
A ganina, wannan manufa ta kasar Sin za ta samar da dama mai muhimmanci ta raya masana'antu a nahiyar Afirka.
To, ko me ya sa nake iya tabbatar da haka? Saboda da farko, kasar Sin mai goyon bayan kasashen Afirka ce a fannin raya masana'antu.
Kasar Sin ta kwashe shekaru fiye da 100 tana kokarin raya bangaren masana'antunta, inda ta sha wahalhalu da matsin lamba iri daya da wadanda kasashen Afirka ke fama da su. Kana bisa kokarin nema, kasar ta samu dabarar bunkasa masana'antu mai dacewa. Saboda haka, dangane da mawuyacin halin da kasashe masu raunin tattalin arziki suke ciki ta fuskar raya masana'antu, kasar Sin tana da wani ra'ayi da ya sha bamban da na kasashen yamma, inda kasar Sin ta kan jaddada muhimmancin raya tattalin arziki da inganta bangaren masana'antu a kasashe masu tasowa. Kana yayin da kasar ke neman raya masana'antunta, tana kuma fatan ganin kasashen Afirka sun samu ci gaba na bai daya, da kawo karshen yanayin koma bayan tattalin arziki, da sarrafawa da cin zarafi da kasashen yamma ke yi musu.
Na biyu shi ne, sabanin yadda kasashen yamma ke kallon tsarinsu a matsayin wanda ya fi kyau a duniya, da yadda suke son ba da umarni ga kasashen Afirka, kasar Sin ta kan samar da dabarar raya masana'antu da ta dace da hakikanin yanayin da kasashen Afirka suke ciki.
Misali, ta la'akari da yadda ake fama da karancin tsare-tsaren da za su taimakawa raya masana'antu, da rashin isassun hanyoyin jigilar kayayyaki a Afirka, kasar Sin ta dauki wasu matakai 3 yayin da take aiwatar da ayyukan hadin gwiwa na raya masana'antu a kasashen Afirka: Da farko ta gina dimbin yankunan masana'antu don tabbatar da gudanar ayyukan manyan ma'aikatu yadda ake bukata. Kana na biyu shi ne, kasar Sin da kasashen Afirka sun kirkiro ayyukan masana'antu masu alaka da kayayyakin more rayuwa da aka gina, don tabbatar da cewa kudin da aka kashe wajen gina kayayyakin more rayuwa na samar da amfani da riba. Yayin da na 3 shi ne, kasar Sin na dora muhimmanci kan zuba jari ga masana'antun samar da kayayyakin da ake bukatarsu a kasuwannin kasashen Afirka, lamarin da ya ingiza tsarin raya masana'antu na kasashen Afirka na mai da hankali kan kasuwannin cikin gida, ta yadda ake tabbatar da ci gaban aikin raya bangaren masana'antu a kai a kai.
Ban da haka, dalili na karshe da ya sa nake sa ran ganin amfanin manufar kasar Sin kan raya masana'antu a Afirka shi ne, kasar ta dade tana samar da fasahohin samun ci gaba ga kasashen Afirka, don ciyar da tattalin arzikinsu gaba ta wata ingatacciyar hanya.
Misali, a shekarun baya, karin kasashen dake nahiyar Afirka sun mai da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani a matsayin sabuwar dabarar neman samun ci gaba, bisa hadin gwiwa da kasar Sin. A kasashen da suka hada da Najeriya da Kenya, da dai sauransu, dandalin biyan kudi ta wayar salula da kamfanoni masu jarin kasar Sin suka kafa na samar da dabarar biyan kudi mai tsaro da sauki ga mutane fiye da miliyan 10. A sa'i daya, kamfanonin kasar Sin sun kaddamar da ayyukan horar da kwararru na fannonin fasahar sadarwa, da ciniki ta yanar gizo ko Internet a kasashen Afirka, inda aka ba dimbin matasan nahiyar Afirka damammaki na koyon fasahohi masu inganci, da wadanda suka shafi kafawa da kula da kamfanoni, ta yadda za a taimakawa kasashen Afirka a fannin zamanantar da fasahohi.
Ta wadannan abubuwa da na bayyana za mu san cewa, kasar Sin na son taimakon kasashen Afirka wajen raya masana'antu, kuma ta san dabara mai dacewa da ya kamata a dauka don taimakawa. Ban da haka, kasar ta dade tana raba fasahohinta masu inganci ga kasashen Afirka, don neman samun ci gaban tattalin arzikinsu na bai daya. Saboda haka, kokarin kasar Sin na raya sabbin fasahohi da sabbin nau'ikan masana'antu tabbas zai samar da damammaki masu kyau na raya tattalin arziki ga kasashen Afirka.
Na kan ji yadda abokaina na Najeriya suke fadin cewa, "A lokacin da kasar Sin ta hau duniyar wata, to, ta tafi tare da Najeriya. " To, idan kun yarda, zan so in gyara maganar, sa'an nan in sanya ta a karshen wannan sharhi, wato: Lokacin da Sin ta hau duniyar wata, tabbas za a samu kasashen Afirka a can, tare da kasar Sin. (Bello Wang)