logo

HAUSA

Kasar Sin ta karyata rahoton da Amurka ta bayar na musanta gudummawar da take bayarwa cinikayyar duniya

2024-02-26 13:49:35 CMG Hausa

Kasar Sin a yau Litinin ta yi kakkausar suka ga wani rahoton da Amurka ta fitar, wanda ya musanta irin gudummawar da kasar Sin ke bayarwa ga tsarin cinikayya da tattalin arzikin duniya, bayan da ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) yau shekaru ashirin da suka gabata.

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kasar Sin a matsayinta na mamba mafi girma kuma mai tasowar tattalin arziki a kungiyar WTO, tana goyon bayan tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, da aiwatar da tsarin hadin gwiwar bangarori dabn-daban da gaske, da cika alkawuran da ta dauka. (Muhammed Yahaya)