logo

HAUSA

Sarki Jordan ya yi gargadin fadada rikicin Gaza a cikin watan Ramadan

2024-02-26 13:31:29 CMG Hausa

Sarkin Jordan Abdallah Na biyu, jiya Lahadi ya yi gargadin cewa ci gaba da yaki a Gaza a cikin watan Ramadan na iya kara fadada yakin.

Sarki Abdallah ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas a birnin Amman, inda ya bukaci da a yi kokarin cimma matsaya na tsagaita bude wuta a zirin Gaza, da kuma kare fararen hula da babu ruwansu, a cewar wata sanarwar da fadar masarautar Hashemi ta fitar.

A cikin wani rahoto kuma, sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 86 tare da raunata wasu 131 a zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu a yankin zuwa 29,692 da jikkata 69,879 tun barkewar rikicin Isra’ila da Hamas a ranar 7 ga Oktobar 2023, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas a cikin wata sanarwar da ta fitar a jiya Lahadi.

Sanarwa ta ce, har yanzu da yawan wadanda abin ya shafa na cikin karkashin baraguzan gine-gine, sakamakon ruwan bama-bamai da kuma rashin jami’an tsaron farar hula da na motocin daukar marasa lafiya. (Yahaya)