logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shirya tsaf domin fara rabon kayan abinci kyauta ga ’yan kasar

2024-02-26 09:16:58 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shirya fara rabon kayan abinci kyauta ga ’yan kasar musamman masu karamin karfi, a wani mataki na saukaka masu wahalhalun da suke fuskanta sakamakon tsada da karancin abinci.

Ministan bunkasa aikin gona da raya birane, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja, ya ce yanzu haka shugaban kasa ya bayar da umarnin fito da tan dubu 42 na kayan abinci daga runbunan ajiyar gwamnati domin rabarwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan ya ce, yanzu an zo gaba ta karshe na fara aikin rabon, inda ya ce, an yi nisa sosai wajen aikin zuba abinci a cikin buhuna wanda daga bisani ne kuma za a damkawa hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar domin ta rabar.

Sanata Abubakar Kyari ya ce, tun bayan lokacin da gwamnati ta sanar da wannan aniya tata na fito da kayan abinci, farashin kayan ya sauko kasa sosai a manyan kasuwannin sayar da kayan abinci dake kasar.

Ya ce, wannan adadi na tan dubu 42 da za a fitar domin rabarwa kyauta daga runbunan ajiya, kari ne a kan tan dubu 60 na shinkafa da gwamnati ta sayo daga kamfanonin sarrafa shinkafa dake kasar.

Ministan gonan na tarayyar Najeriya ya ci gaba da cewa, domin bunkasa sha’anin samar da abinci a cikin gida, nan gaba kadan za a fara aiwatar da shirin noman rani a dukkan jihohin kasar 36 cikin har da birnin Abuja, inda za a noma Shinkafa da Masara da Alkama da kuma Rogo, kuma akwai tallafi mai yawa ga manoman da za su gudanar da wannan aiki.

“Manomi zai biya kudin rabin taki ne kawai, amma kuma za a ba shi buhu uku na takin, kamar yadda aka tsara shirin bunkasa noma na kasa zai dauki nauyin biyan kudin buhu daya da rabi, manomi kuma zai biya kudin rabi yayin da kuma ma’akatar harkokin noma ta tarayyar ta karkashin shirinta na bayar da tallafi za ta biya kudin buhu guda, kuma dukkan wannan ya kunshi maganin kwari da shi kansa irin shuka wanda shi ma kyauta ne.” (Garba Abdullahi Bagwai)