Lu Yutong: Taimakawa kasar Sin wajen cimma gagarumar nasara a bangaren samar da Supercomputer a duk fadin duniya
2024-02-26 14:40:54 CMG Hausa
Lu Yutong, daraktar cibiyar samar da kwamfutocin sarrafa bayanai ko lissafi da saurin gaske wato Supercomputer ta Guangzhou dake lardin Guandong na kudancin kasar Sin, kuma farfesa a kwalejin nazarin kimiyyar kwamfuta da Injiniya a jami’ar Sun Yat-sen. Lu ta sadaukar da kanta wajen taimakawa kasar Sin cimma gagarumar nasara na tsawon shekaru 10 a bangaren samar da kwamfutocin sarrafa bayanai da saurin gaske a duk fadin duniya. An nada Lu a matsayin shugabar kula da shirye-shriye na babban dandalin taro na ISC High Performance na shekarar 2019, wadda ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko kuma basiniya ta farko, masaniyar kimiyya da ta kasance shugabar kula da shirye-shriye na babban dandalin.
Supercomputing, wani ingantaccen tsarin lissaffa bayanai ko alkaluma da saurin gaske ne da ke amfani da ma’aunin da ake kira flops wajen bayyana adadin bayanai da ake lissaffawa cikin ko wace dakika. Idan aka dauki kwamfuta kirar Tianhe-2 a matsayin misali, to tana iya lissaffa bayanai 33.86 petaflops, kwatankwacin quadrillion 33.86 cikin ko wace dakika. Kuma tana iya adana bayanai masu tarin yawa. Idan za a yi amfani da kwamfuta kirar Tianhe-2 wajen adana littattafan Intanet, to za ta iya adana kimanin littattafan biliyan 100, wadanda kowannensu ke da kalmomi 100,000.
Ana amfani da irin wannan tsarin lissafi a bangarori da dama, kamar bangaren likitancin da ya hada da nazarin halittu da sinadarai, da jiragen sama, da layin dogo mai saurin tafiya, da fasalin masana’antu, da hasashen yanayi. Ita ma kirkirarriyar basira wato AI dake samun karbuwa na amfani ne da irin wannan tsari da aka samo daga Supercomputer.
Kasashe da dama na ba bangaren ci gaban tsarin sarrafa bayanai ko lissafi da saurin gaske muhimmanci matuka. Kasar Sin tana daukar batun inganta bangaren a matsayin wata alkibla mai muhimmanci wajen raya bangarenta na kimiyya da fasaha. Yanzu, tsarin lissafi na Supercomputing na kasar Sin, na daya daga cikin wadanda ke kan gaba a duniya. Cibiyar da Lu Yutong ke ciki kuma tana cikin cibiyoyin samar da irin wadannan kwamfutoci mafiya tasiri guda biyar a duniya.
Lu ta jagoranci abokan aikinta wajen cimma muhimman sakamakon kirkire-kirkire da dama da nasarori a bangaren. Cibiyar tana samarwa mutane daga dukkan bangarorin rayuwa damar samun hidimomin irin wannan tsarin lissafi. A ganin Lu, tsarin lissafin Supercomputing, ba muhimmi ne a bangaren binciken kimiyya kadai ba, har ma da hidimtawa rayuwar jama’a ta yau da kullum.
Iyayen Lu Yutong ne suka karfafa mata gwiwar raya dabi’ar karatu tun tana karama. Tana son karatun almaran kimiyya da tsatsuniyoyi. Mahaifinta ya karfafa mata gwiwar karanta littattafan da take sha’awa, ba na karatun makarata kadai ba.
Lu ta bayyana cewa, “iyayena sun aminta da ni, kuma ‘yancin da suka ba ni, ya ba ni damar yin aiki a bangaren da nake matukar kauna. Ilimin ya min amfani, kuma zai ci gaba da yi min amfani har karshen rayuwata.” Ta kuma kara da cewa, “a lokacin da nake makarantar sakandare, na shiga cikin wasu shirye-shirye masu kayatarwa bayan na tashi daga makaranta, kuma na karanta littattafai mafi yawa a wadannan shirye-shiryen, wadanda suka taimaka min kwarai. A wannan lokaci, na iya lissafi sosai. Ina jin sha’awata dangane da kimiyya sun samo asali ne tun a sakandare.”
A shekarar 1983, an samar da kwamfutar sarrafa bayanai da saurin gaske wato Supercomputer kirar Yinhe-1 a jami’ar fasahohin tsaro ta kasar Sin ta NUDT dake lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, wadda saurinta na sarrafa bayanai ya kai flop miliyan 100. Lamarin da ya kai kasar Sin ga zama kasa ta 3 bayan Amurka da Japan dake iya samar da irin wadannan kwamfuta.
A lokacin, Lu Yucheng tana ajin farko a babbar makarantar sakandare, ita da abokan karatunta sun samu damar ziyartar wannan kwamfutar. Lu ta bayyana cewa, “girman kwamfuta kirar Yinhe-1 ya yi kama da wani dan karamin dakin taro. Wayoyin laturoni ne suka mamaye samansa. Kwamfuta mai girman hakan ta ja hankalina sosai. Daga bisani, na kara fahimtar muhimmancinta. Don haka, na kuduri niyyar gudanar da binciken kimiyya a nan gaba. An sanya ni a kwalejin nazarin kimiyyar kwamfuta dake karkashin jami’ar NUDT, bayan na kammala babbar makarantar sakandare.”
Lu ta kara da cewa, “a wancan lokaci, ban yi tunanin zan zama masaniyar kimiyya ba. Amma dai, ina ganina a matsayin mai tsara manhajoji maimakon masaniyar kimiyya. Kawai dai ina fatan yin
abun da ya kamata in yi, tare da bayar da gudumnmuwata ga al’umma, ba tare da la’akari da kankanta ko girmanta ba. Ina fatan amfanawa kasata da kuma al’umma.” Lu Yutong ta shiga aikin samar da samfura biyu na kwamfutar Yinhe bayan ta kammala karatu a jami’ar NUDT. Daga nan ta samu damar da kwamitin bayar da tallafin karatu na kasar Sin ta samar, ta ci gaba da karatu a kasar waje. Sai dai, kasar Sin ta yi niyyar sabunta tsarin kwamfutar Yinhe, don haka a matsayinta na jagorar tawagarta, Lu ta hakura da damar na yin karatu a kasar waje. Tun daga sannan kuma, ta shiga aikin samar da samfura da dama na Kwamfutocin Yinhe, da kuma samfura biyu na Kwamfutocin Tianhe.
Lu ta bayyana cewa, “da farko, kasar Sin tana bin bayan manyan kasashe a masana’antar samar da irin wadannan kwamfutar sarrafa bayanai da saurin gaske na Supercomputer. Sai kuma ta cimma su, har ma a yanzu, muka zarce su. Ban taba da-na-sanin hakura da damata ta fita kasar waje karatu ba. Na shaida tare da bayar da gudummuwa ga nasarar da Sin ta samu cikin sauri a masana’antar.” (Kande Gao)