logo

HAUSA

An kaddamar da wata kungiyar ’yan makaranta ta AES tare da zaben dan Nijar a matsayin shugaban kungiyar

2024-02-25 15:02:40 CGTN HAUSA

 

A ranar jiya Asabar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2024, birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso ya karbi bakuncin bikin kaddamar da kungiyar ’yan makaranta ta AES, inda ’yan makaranta da dalibai na kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso suka kafa kungiyar tare da zaben dan Nijar a matsayin shugaban wannan sabuwar kungiya.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.