Jami’in Isra’ila: Isra’ila da Palasdinu za su kara tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2024-02-25 16:08:23 CGTN HAUSA
Wani jami’in Isra’ila da ba a bayyana sunansa ba, ya shaidawa manema labarai na kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Isra’ila za ta tura tawagarta zuwa birnin Doha, hedkwatar Qatar, don gudanar da sabon zagayen shawarwari kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Palasdinu.
Wannan jami’i ya ce, a jiya Asabar, majalisar ministocin Isra’ila a lokacin yaki, ta saurari ci gaban da aka samu a sabon zagayen shawarwarin da aka yi, daga baya kuma ta yanke shawarar tura tawagar kananan jami’ai zuwa Doha a kwanaki masu zuwa, don kara tattaunawa a bangaren jin kai na yarjejeniyar.
Kafar yada labarai ta Palasdinu ta ba da labari a jiyan cewa, sojojin Isra’ila sun kai hare-hare masu yawa ta sama a wasu birane biyu dake kudancin zirin Gaza, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 15.
Hukumar kiwon lafiyar Palasdinu dake zirin Gaza, ta gabatar da kididdiga a jiya cewa, hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai sassan zirin a cikin awoyi 24 da suka gabata sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 92, yayin da wasu 123 suka ji rauni. (Amina Xu)