Jakadan Sin a Girka ya yi kira da a karfafa alakar raya tattalin arziki tsakanin Sin da EU
2024-02-25 16:28:40 CMG Hausa
Jakadan kasar Sin a kasar Girka Xiao Junzheng, ya jaddada muhimmancin bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen Turai da Sin, kana su karfafa hadin kai sama da batun takara.
Jakada Xiao, wanda ya yi wannan tsokaci ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Athens, ya yi karin haske game da muhimmancin hadin gwiwa, bayan taro karo na 5 na kasashen kudu maso gabashin Turai da na bahar Aswad, wanda ya hallara wakilai 170 daga hukumomin kasa da kasa, da gwamnatoci, da jami’an diflomasiyya da ‘yan kasuwa.
Mahalarta taron sun tattauna ne a makon jiya, game da batutuwan siyasar shiyyoyi, da hadin gwiwar yanki, a birnin Athens na Girka.
A cewar jakada Xiao, kamar Turai, ita ma kasar Sin ta kirkira, ta ci gajiya, kana tana bayar da kariya ga odar cudanyar kasa da kasa. Kaza lika Sin da Turai na goyon bayan baiwa sassa daban daban na duniya damar yin tasiri, tana adawa da tsarin kafa gungun fito na fito, da sabon yakin cacar baka, da warewa, da gurgunta tsarin shigar da hajojin bukata zuwa sassan kasa da kasa.
Game da shawarar nan ta ziri daya da hanya daya ko BRI, jakada Xiao ya ce Sin ba ta adawa, da shirin raya ababen more rayuwa na kasa da kasa wanda kungiyar EU ta kirkiro.
Bugu da kari, jakadan ya ce Sin da Turai na iya zurfafa daidaito bisa matsayin koli, ta yadda za su kara goyawa juna baya wajen bunkasa fifikon su, da hada gwiwa a harkokin nahiyar Afirka, ta yadda hakan zai bunkasa ci gaban duniya baki daya. (Saminu Alhassan)