Sin Ta Yi Kira Da A Warware Rikicin Ukraine A Siyasance
2024-02-24 16:01:20 CMG Hausa
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga kasashen duniya da su yi kokarin warware rikicin kasar Ukraine a siyasance.
Zhang Jun, ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su hada kai, don samar da hanya mai adalci da ta dace, ta yadda za a iya warware rikicin ta hanyar siyasa, da kuma samun zaman lafiya.
Ya yi wannan roko ne, a wani babban taron kwamitin sulhu na MDD da aka shirya jiya Jumma’a, albarkacin cika shekaru biyu da Rasha ta kaddamar da aikin soji na musamman a Ukraine.
Ya ce, bai kamata bangarorin da abin ya shafa su kirkiro wani abu da zai haifar da cikas ga kokarin samun zaman lafiya ba, kana bai kamata a samar da makamai don samun riba daga rikicin mai tsawon lokaci ba.
Wakilin na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta da hannu a rikicin Ukraine, haka kuma kasar Sin ba ta cikin rikicin. Amma duk da haka, kasar Sin ba ta nuna halin ko-in-kula ga rikicin ba, ba ta samu riba daga rikicin ba.
Dangane da batun Ukraine, Zhang ya ce, kasar Sin ta ci gaba da kiyaye cewa, ya kamata a mutunta ikon mallakin kai na kasa da cikakkun yankunan dukkan kasashen duniya, da kiyaye manufofi da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD, bisa la'akari da yanayin tsaron da ya dace na dukkan kasashen duniya, da duk wani kokarin da ake yi na tabbatar da sulhu da goyon bayan warware rikicin cikin lumana.
A yayin wannan taro, shi ma babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kawo karshen rikicin Ukraine.
Ya ce, a zahiri hadarin rikice-rikicen da ke kara ta'azzara na fadada. A duk duniya, rikicin Ukraine yana kara rarrabuwar kawuna na siyasa, baya ga haifar da rashin zaman lafiya a yankin, da rage fatan da ake da shi na magance wasu batutuwan da suka shafi duniya cikin gaggawa, da kuma lalata ka'idoji da dabi'un bai daya da ke tabbatar da tsaro a duniya, Yana mai cewa, makomar wannan rikici da zai haifar da hadarin nukiliya tana sanyaya zukata a sassan duniya.(Ibrahim)