Hukumar kwastam a Najeriya ta kaddamar da shirin sayarwa al’ummar kasar shinkafa da sauran kayan abinci da ta kama daga masu fasa-kauri
2024-02-24 15:02:52 CMG Hausa
Hukumar kwastam a tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirinta na sayar da shinkafa da sauran kayayyakin abinci da ta kama daga hannun masu fasa-kauri ga al’ummar kasar a kan farashi mai rahusa Naira dubu 10 kan kowanne kilogram 25.
Shugaban hukumar Adewale Adiniyi ne ya sanar da kaddamar da shirin a hedikwatar shiyya ta hukumar dake Yaba a jihar Legos, inda ya ce, an yanke shawarar fito da shinkafar ce domin rage matsalolin karancin abinci da al’ummar kasar ke fuskanta.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaban hukumar ta kwastam ya ce, a daidai lokacin da gwamnatin ke ta fadi tashin shawo kan kalubalen da tattalin arzikin kasar ke fuskanta, wanda ya samo tushe daga matsalolin tsoro da kuma batun musayar kudaden waje, amma kuma wasu marasa kishin kasa ke amfani da wannan dama wajen fasa-kaurin kayayyakin abincin da ake samarwa a kasar zuwa kasashe makwafta.
Irin wadannan kayayyakin abincin ne da jami’an hukumar suka kama, aka yanke shawara a gwamnatance a fito da su domin sayarwa ga jama’a. Ya ce, ba shinkafa ce kawai aka kama ba, har da Wake, da Masara, da Gyero, da Dawa da Waken Soya da Macaroni da Sikari da sauran kayan girki kamar Mai da kuma Gishiri.
Ya jaddada kudurin hukumar ta kwastam cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kan iyakokin kasar daga masu fasa-kaurin kayayyaki zuwa cikin gida ko kuma fitarwa zuwa kasashen waje, inda ya ce, za a kaddamar da sayar da irin wadannan kayayyaki da aka kama a sauran ofisoshin shiyya na hukumar dake sassan kasar daban daban.
“Domin tabbatar da ganin an kare yin kwana da wadannan kayayyaki ko saba ka’idar sayar da su ga jama’a, mun samar da sharododi da dokoki da za su tabbatar da ganin masu tsananin bukata ne kawai za a sayar kayan abincin.”
Haka kuma ya ce, an dauki tsararan matakai na hukunci ga duk wani jami’in hukumar kwastam da aka kama yana yin karan tsaye ga samun nasarar wannan shiri, wanda ake da tabbacin zai rage karancin abinci a cikin kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)