logo

HAUSA

Shekaru 2 Ke Nan Da Barkewar Rikici A Tsakanin Rasha Da Ukraine

2024-02-23 22:04:58 CMG Hausa

A ranar 24 ga wata ne za a cika shekaru 2 da barkewar rikici tsakanin kasashen Rasha da Ukraine. Yanzu sojojin kasashen 2 na cikin tsaka mai wuya. Kasashen Amurka da Turai suna shirin kakabawa Rasha sabbin takunkumi. Ya zuwa yanzu babu alamar kawo karshen rikicin. Akasarin ra’ayoyin kasa da kasa sun takaita babbar asarar da rikicin ya haifar, tare da yin tunani mai zurfi kan dalilin da ya haddasa barkewar rikicin, da kuma yin kira a tsagaita bude wuta.

Rikicin Rasha da Ukraine shi ne yaki mafi muni da ya barke a nahiyar Turai bayan yakin cacar baka. Bisa kididdigar da hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD ta fitar, a cikin shekaru biyu da suka gabata, yawan mutanen Rasha da Ukraine da suka mutu da jikkata ya kai sama da dubu 500 yayin da sama da 'yan Ukraine miliyan 10 suka rasa matsugunansu. Barkewar rikicin ya haifar da hauhawar farashin makamashi da abinci a duniya, a wasu kasashen Afirka kuma, an gamu da matsalar karancin abinci.

Yayin da ake sake tunanin rikicin yanzu, an kara fahimtar cewa, siyasar kasa da kasa, ba abu mai sauki ba ne. Ra’ayin yakin cacar baki shi ne dalilin da ya haifar da rikicin. Amurka kuma tana yunkurin yin fito-na-fito. Haka kuma, sanya takunkumin kashi kai ba shi da amfani, illa rura wuta kawai.

Bugu da kari, wannan rikici da aka shafe tsawon shekaru biyu ana yi, ya kuma tabbatar da cewa takunkumin da aka sanya wa hannu bai yi tasiri ba, sai dai yana kara zafafa rigingimu da fadace-fadace. Kwarewar tarihi ta tabbatar da cewa karshen kowane rikici shi ne komawa teburin tattaunawa.

Yadda aka dauki tsawon lokaci ana rikici tsakanin Rasha da Ukraine, an kuma kara sarkakiyyar rikicin da fadada rikicin, bai dace da moriyar kasashen duniya ba. Ba yadda za a yi sai a yi tattaunawa da shawarwari. Tilas ne a yi adalci da kai zuciya nesa da nuna daidaito kan ikon mulkin kan Ukraine da tsaronta da kuma damuwar Rasha ta fuskar tsaro. (Tasallah Yuan)