logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi kira ga SCO da ta kasance “jigon daidaito” a yanayin tangal-tangal da sauye-sauye

2024-02-23 10:19:48 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kamata ya yi dukkan mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) su hada kai wajen neman bunkasuwar kungiyar tare da mayar da ita ginshikin daidaita sauye-sauyen duniya.

Wang, wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin Kolis JKS, ya bayyana hakan ne a yayin wani liyafa da aka yi a nan birnin Beijing, domin murnar cika shekaru 20 da kafa sakatariyar SCO. 

Wang ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da dukkan bangarori domin tabbatar da cewa, taron koli na Astana na bana ya samar da sakamako mai kyau, da samar da sabbin damammakin raya kungiyar SCO, da kara ba da gudummawa ga dauwamammen zaman lafiya da wadata a duniya baki daya. 

A cikin shekaru 20 da suka gabata, kungiyar SCO ta bunkasa daga kasashe shida zuwa babban iyali mai kasashe mambobi 26, da masu sa ido da abokan huldar tattaunawa, da samar da sabon tsarin hadin gwiwa dake nuna hadin kai, bayyana gaskiya, samun nasara, da fahimtar juna tsakanin kasashe masu tsarin zamantakewa da hanyoyin ci gaba mabambanta, a cewar Zhang Ming sakatare-janar na kungiyar SCO. 

Sama da mutane 200 da suka hada da wakilan diflomasiyya na kasashen SCO da wakilan kungiyoyin kasa da kasa a kasar Sin ne suka halarci liyafar. (Muhammed Yahaya)