‘Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun dauki alhakin kai hari kan jirgin ruwan dakon kaya na Burtaniya a mashigin tekun Aden
2024-02-23 10:57:19 CMG Hausa
Kungiyar mayakan Houthi ta Yemen ta dauki alhakin kai hare-haren makamai masu linzami kan wani jigin ruwan dakon kaya na kasar Burtaniya da ke gabar tekun Aden a ranar Alhamis.
Kakakin rundunar mayakan Houthi Yahya Sarea a cikin wata sanarwar da tashar talabijin ta kungiyar ta al-Masirah ta watsa ya ce, “Dakarun kungiyar na ruwa sun kai hari kan wani jirgin ruwan Burtaniya mai suna Islander a mashigin tekun Aden da makamai masu linzami da dama. Makaman masu linzami sun sauka kan jirgin inda kuma ya kama da wuta, “Mun kuma kai hari kan wani jirgin ruwan yakin Amurka a bahar Maliya da jirage marasa matuka,” a cewar Sarea.
Ya kara da cewa, kungiyarsa ta kuma harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka zuwa birnin Eilat na kasar Isra'ila.
Wannan dai shi ne hari na baya bayan nan na hare-haren Houthi tun tsakiyar watan Nuwambar bara domin nuna goyon baya ga Hamas. (Yahaya)