logo

HAUSA

Wakilin Sin: Ya zama wajibi a tsagaita bude wuta a Gaza

2024-02-23 10:40:58 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya ce ya zama wajibi a dakatar da bude wuta a Gaza nan take, yana mai cewa, aikin kowanne matakin Kwamitin Sulhu shi ne, cimma dakatar da bude wuta nan take.

Hawa kujerar naki da Amurka ta yi kan kudurin da Algeria ta gabatar a ranar Talata na nufin Kwamitin Sulhu na MDD ya sake rasa wata dama ta ingiza dakatar da bude wuta a Gaza. Zhang Jun ya bayyana a jiya cewa, dakatar da bude wuta a Gaza abu ne da ya zama wajibi domin ceton rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba da kare bazuwar yaki.

Ya ce kasar Sin na fatan Amurka za ta nuna sanin ya kamata, ta amsa kiran kasashen duniya, ta kuma martaba matsayar da mambobin kwamitin sulhun suka cimma.

Har ila yau, ya ce akwai bukatar kawo karshen wahalhalun da Falasdinawa suka dade suna sha. Kuma dole ne a tabbatar da burin Falasdinun na zama mai cin gashin kanta. Ya ce Sin na goyon bayan Falasdinu ta zama mamban MDD nan bada jimawa ba, kuma Sin din na kira da a gudanar da taron tattaunawa kan batun zaman lafiya na kasa da kasa dake da karfin iko da girma da tasiri, domin lalubo mafita mai dorewa da adalci ga batun Falasdinu. (Fa’iza Mustapha)