’Yan sanda sun bankado wata kungiyar masu fataucin makamai da miyagun kwayoyi a Dakoro dake yankin Maradi
2024-02-22 10:40:15 CMG Hausa
A jamhuriyyar Nijar, ’yan sandan jihar Dakoro dake yankin Maradi sun bankado wani gungun masu fataucin makamai da miyagun kwayoyi da kuma aka mika su zuwa ga hukomomin wurin a ranar jiya Laraba 21 ga watan Fabrairun shekarar 2024.
Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya turo mana wannan rahoto. //////
Su dai makaman da aka kama sun kunshi bindigogi 6 da suka hada da AK 47 guda da kuma PA guda 6, da harsasai guda 18, da mota guda kirar V8, da babura guda 4 da kuma kilo biyu na tabar wiwi. An kama mutum 4 dake cikin gungun mai kunshe da mutane 15 wanda daga cikinsu yawanci sun shiga hannun ’yan sanda, a cewar Mohamed Souleymane darektan ’yan sanda na jihar Dakoro.
Ferefen jihar Dakoro kaftin Amadou Garba ya jinjinawa kokarin kwamishinan ’yan sanda tare da mutanensa bisa ga jajircewar da suka nuna wajen kama wadannan miyagun mutane da kuma tabbatar da tsaron jama’a da dukiyoyinsu, tare da kiransu da suka kara rubanya kokari da kuma yi musu alkawarin kayan aiki da suka dace domin aikinsu ya je gaba, ta yadda al’umma za ta kwanta lafiya ta tashi lafiya, a cewar Kaftin Amadou Garba.
A nasa bangare, shugaban kotun jihar Dakoro, Boulama Maman Madaka ya tabbatar da cewa tuni wadannan miyagun mutane za su amsa laifinsu gaban kotu.
Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.