logo

HAUSA

Cote d’Ivoire ta shirya bada tabbaci ga kayayyakin more rayuwa da aka yi amfani da su a yayin gasar AFCON

2024-02-22 21:36:26 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Cote d’Ivoire, ta sanar a kwanakin baya cewa, ana shirin kafa wata hukuma ta musamman don sa lura da bada tabbaci ga kayayyakin more rayuwa da aka yi amfani da su a yayin gasar cin kofin Afirka wato AFCON ta shekarar 2023, ta yadda kayayyakin za su ci gaba da samar da hidimomi a sha’anin wasan kwallon kafa a kasar Cote d’Ivoire har ma ga duk nahiyar Afirka.

Shugaban hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Cote d’Ivoire Augustin Sidy Diallo ya bayyana cewa, hukumar ta bada shawarar mai da biranen da suka dauki bakuncin gudanar da gasar AFCON a wannan karo a matsayin birane masu martaba ta biyu da aka dorawa muhimmanci wajen raya su, tare da kafa asusun musamman na raya wasan kwallon kafa tsakanin matasa da yara a kasar.

A gun bikin murnar cimma nasarar lashe kofin AFCON da kungiyar wasan kwallon kafa ta Cote d’Ivoire ta yi a shekarar 2024 da aka gudanar a kwanakin baya, shugaban kasar Alassane Ouattara ya bayyana cewa, aikin dake gaban komai a halin yansu shi ne kiyaye abubuwan more rayuwa na gasar AFCON.

A matsayin kasar da ta karbi bakuncin gudanar da gasar cin kofin Afirka wato AFCON a wannan karo, kasar Cote d’Ivoire ta zuba jari kudin yammacin Afirka wato FCFA biliyan 900, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 479, wajen gina kauyen ‘yan wasa masu halartar gasar AFCON, da hanyoyin motoci, da otel, da filayen wasa shida. A cikinsu, kasar Sin ta taimaka wajen gina filin wasa mafi girma wato filin wasan Olympics na Abidjan, wanda ke iya dauka ‘yan kallo dubu 60 a sa’i daya.


Kocin wucin gadi na kungiyar Cote d’Ivoire ya kasance koci mafi hazaka a gasar AFCON a wannan karo

Bayan da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Cote d’Ivoire ta lashe kofin Afirka wato AFCON karo na 34, kocin wucin gadi na kungiyar Emerse Faé, ya kasance koci mafi hazaka a gasar AFCON ta wannan karo.

A gasar AFCON a wannan karo, kungiyar Cote d’Ivoire ta fuskanci kalubale, a wasan rukuni, kungiyar ta ci tura sau biyu, ta kuma tsaya a matsayi na uku a rukunin ta kafin ta kai zagaye na biyu. Amma wannan bai hana kungiyar ta samu nasara ba. Sai dai kungiyar ta tabbatar da samun nasarori, kana ta doke kungiyar Super Eagles ta Nijeriya a wasan karshe na gasar, ta kuma lashe kofin gasar AFCON a karo na uku.

A tarihin gasar AFCON, kungiyar Cote d’Ivoire ta zama kungiya ta farko da ta lashe kofin bayan ta ci tura sau biyu, a wasannin rukuni, kana aka kori kocin kungiyar a yayin gasar.

Haka zalika kuma, an baiwa dan wasan kungiyar Super Eagles Nijeriya William Troost-Ekong, lambar yabo ta dan wasa mafi hazaka a gasar ta AFCON a wannan karo, kuma dan wasan kungiyar Equatorial Guinea Emilio Nsue ya ci kwallaye biyar a yayin gasar ta AFCON, inda ya samu lambar yabo ta dan wasa mafi zura kwallaye a raga. Sai kuma dan wasan kungiyar Afirka ta Kudu Ronwen Williams, wanda ya zama mai tsaron gida mafi kwazo. Akwai kuma dan wasan kungiyar Cote d’Ivoire Simon Adingra, wanda ya zama matashin dan wasa mafi kwarewa, kuma kungiyar Afirka ta Kudu ta zama kungiya mai fafatawa a gasar mafi adalci a wannan karo.


Dan wasan gudun Marathon Kelvin Kiptum ya rasu a sakamakon hadarin mota

Bisa labarin da hukumar kula da harkokin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta bayar, an ce, dan wasan gudun yada-kanin-wani na Marathon na kasar Kenya, wanda ya kiyaye bajimtar duniya a wasan a halin yanzu Kelvin Kiptum ya rasu, a sakamakon hadarin mota a daren ranar 11 ga wannan wata a kasar Kenya, Kiptum ya rasu yana da shekaru 24 a duniya.

Hadarin motar ya abku ne a kan hanyar dake tsakanin birnin Eldoret da Kaptagat, kana kocinsa Gervais Hakizimana shi ma ya rasa ran sa a sakamakon hadarin.

An haifi Kelvin Kiptum a ranar 2 ga watan Disamba na shekarar 1999 a kasar Kenya, kuma ya fara horon gudu a yayin da yake da shekaru 13 kacal. Tun daga shekarar 2019, Kiptum ya fara shiga gasannin kasa da kasa, kuma sau da dama ya sha kammala gudun rabin zangon Marathon a kasa da sa’a daya. Bayan da ya fara shiga gasar Marathon, ya fara jawo hankulan jama’a sosai.

A watan Disamban shekarar 2022, Kiptum ya halarci gasar Marathon a birnin Valencia na kasar Spaniya, inda ya gama gasar cikin awa 2 da minti 1 da dakika 53, kuma wannan ne karo na farko da ya halarci gasar gudun Marathon, kana ya zama dan wasa mafi sauri a duniya da ya halarci gasar gudun Marathon a karo na farko. A gasar gudun Marathon ta London da aka yi a watan Afrilun shekarar 2023, ya kammala tseren cikin  sa’a 2 da minti 1 da dakika 25, inda ya kammala a matsayi na biyu a duniya, wato saura dakika 16 ya kai ga cimma bajimtar duniya a wasan.

Sai dai bayan watanni 6 da kammala gasar gudun Marathon ta Chicago, Kiptum ya kammala tsere cikin sa’a 2 da dakika 35, inda ya karya bajimtar duniya a wasan, kuma ya kasance dan wasa na farko da ya kammala tsere a kasa da awa 1 da minti 1 a gasar gudun Marathon a duniya a tarihi.

A karshen shekarar 2023, hukumar kula da harkokin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta bayar da lambar yabo ga Kiptum, sakamakon yadda ya zamo dan wasa mafi kwarewa na shekarar 2023 a gasannin kasa da kasa da aka gudanar.

Bayan da ya karya bajimtar duniya, Kiptum bai ci gaba da halartar gasar gudun Marathon ba. Bisa shirinsa na halartar gasar gudun Marathon ta birnin Rotterdam a watan Afrilun shekarar bana, inda zai yi kokarin kammala tsere cikin sa’a 2. To sai dai rasuwar sa ta katse wannan buri, kuma lamarin ya tabbatar da kammalar damarsa ta halartar gasannin gudun Marathon guda uku kacal.

Shugaban hukumar kula da harkokin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya Sebastian Newbold Coe, ya nuna bakin ciki ga rasuwar Kiptum da kocinsa, ya bayyana cewa, dan wasan ya ajiye tarihi mai ban al’ajabi, ya ce “Dukkanmu za mu tuna da shi sosai”.


Kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympics ta Brazil ta gaza samun iznin shiga gasar wasannin Olympics ta Paris

A zagayen karshe na neman shiga gasar wasannin Olympics na nahiyar kudancin Amurka da aka yi a birnin Caracas dake kasar Venezuela a kwanakin baya, kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympics ta kasar Brazil, ya ci tura a hannun kungiyar Argentina da ci daya da nema, don haka kungiyar Brazil wadda ta zama zakara a gasar wasannin Olympics a karo biyu da suka gabata, a wannan karo ta gaza samun gurbin shiga gasar wasannin Olympics ta Paris.

A sauran wasannin zagayen karshe, kungiyar Paraguay ta doke kungiyar Venezuela da ci biyu da nema, don haka kungiyar Paraguay da kungiyar Argentina, su biyu sun samu damar shiga gasar wasannin Olympics ta Paris.

Game da hakan, kocin kungiyar Brazil Mano Menezes, ya bayyana cewa, sun yi takaici sosai sakamakon gaza cimma burinsu.