logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ci burin samar da dala biliyan 10 domin farfado da darajar kudin kasar

2024-02-22 10:09:20 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce, tana fatan samar da dala biliyan goma domin farfado da hada-hadar kasuwancin kudaden waje ta yadda darajar kudin kasar za su yi kima sosai.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja yayin kaddamar da taron wakilan hukumar daraktocin sashen lura da kaddarori da harkokin zuba jari na gwamnati. Ya ce. gwamnati ba za ta ci gaba da zuba ido darajar Naira na ci gaba da tabarbarewa ba a duniya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Mataimakin shugaban kasar ya ce, baya ga yunkurin daidaita farashin kudaden waje, gwamnati na da shirin samar da miliyoyin guraben ayyukan yi ga ’yan kasa ta hanyar farfado da ayyukan kamfanoni da cibiyoyin hada-hada mallaki gwamnati da suka jima ba a yi amfani da su ba, wanda yin hakan zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin cikin gida.

Sanata Kashim Shettima ya ce, akwai kaddarorin gwamnatin Najeriya na biliyoyin Naira warwatse a cikin gida da kuma kasashen ketare wanda an shafe shekaru masu yawa ba a waiwaye su ba, lamarin da ya haifar da asara mai dinbin yawa na kudin shiga, hakan kuma ya shafi ci gaba tattalin arzikin kasa sosai.

Mataimakin shugaban kasan ya ce, duk da haka gwamnati sai ta dauki managartan matakai da za su rage tasirin kudaden waje a kan Naira.

“Kwanan nan gwamnatin tarayya ta dora danbar samar da a kalla dala biliyan goma domin a samu yalwa a kasuwar hada-hadar kudaden waje, yin hakan babban sinadari ne da zai kyautata darajar Naira da kuma bunkasar tattalin arziki.”

Daga karshe, Sanata Kashim Shettima ya bukaci ma’aikatu da cibiyoyin bunkasa hada-hadar kudi da sauran hukumomi masu zaman kansu da su hada kai da hukumar daraktocin sashen lura da kaddarori da jarukan gwamnati wajen tabbatar da ganin ’yan kasa na cin gajiyar arzikin gwamnati domin samun makoma ingantacciya. (Garba Abdullahi Bagwai)