logo

HAUSA

Blinken: Idan Ba Ka Da Karfi, Za A Cinye Ka

2024-02-22 15:31:50 CGTN HAUSA

DAGA MINA

“A tsarin duniya, idan ba ka da karfi, to za a cinye ka”. Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ne ya yi wannan magana a zauren tattaunawa tsakanin rukuni-rukuni na taron tsaro na Munich da aka gudanar a kwanan baya. Abin da ya bayyana matsayin da ‘yan siyasar Amurka ke daukawa na matukar son fin karfi da babakere yayin da suke daidaita harkokin duniya, abin ban tsoro kuma mamaki.

A halin yanzu duniya na la’akari da ra’ayin bangarori daban-daban, hadin kai da samun bunkasuwa tare, wanda hakan ya fi dacewa da   makomar Bil Adama baki daya. Manufar babakere wadda ta keta muradun sauran kasashe don raya wata kasa kawai ba ta dace da yanayin da ake ciki ba. Yaushe Amurka za ta yi watsi da tunanin wani bangare daya dake samun riba da matukar fin karfi da babakere, ta rungumi ra’ayi na hadin kai da samun moriya tare? (Mai zana da rubutu: MINA)