logo

HAUSA

Fadar shugaban Falasdinu da Hamas sun yi Allah wadai da kuri’ar kin amincewar Amurka ta tsagaita bude wuta a Gaza

2024-02-22 10:21:28 CMG Hausa

A jiya Laraba ne fadar shugaban Falasdinu da kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas suka yi Allah wadai da kuri’ar kin amincewar Amurka ta tsagaita bude wuta a zirin Gaza.

A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA ya fitar, fadar shugaban Falasdinu ta bayyana mamakinta kan yadda Amurka ke ci gaba da kin dakatar da yakin da Isra’ila ke yi da al’ummar Falasdinu.

Sanarwar ta ce, “Matakin da Amurka ta dauka na kin amincewa da bukatar kasashen duniya, za ta ba da karin dama ga Isra’ila don ci gaba da kai munanan hare-haren kan al’ummarmu a zirin Gaza, da Rafah”.

A dayan bangaren kuma, kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, gwamnatin Amurka ce ke da alhakin kawo cikas ga kokarin kawo karshen hare-haren Isra’ila a Gaza.

Amurka ta ba da "dama ga Isra'ila don kashe mutanenmu marasa tsaro ta hanyar jefa musu bama-bamai da yunwa, kuma da hannunta a cikin yakin." a cewar sanarwar Hamas. (Yahaya)