logo

HAUSA

A kalla ’yan Nijar bakin haure 141 dake zaune a Libiya suka iso birnin Yamai

2024-02-21 10:04:28 CMG Hausa

A ranar jiya Talata 20 ga watan Fabrairun shekarar 2024, wani jirgin sama dauke da ’yan Nijar 141 akasarinsu matasa dake kasar Libiya matsayin bakin haure ya sauko a filin jiragen sama na Diori Hamani dake birnin Yamai.

Daga birnin Yamai din abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

A kalla su 141 ’yan Nijar dake a matsayin bakin haure dake zaune a kasar Libiya da ba su da cikakkun takardun zaman kasa suka dawo Nijar, bayan an kwaso su zuwa birnin Yamai a ranar jiya 20 ga watan Fabrairun shekarar 2024.

Aikin jigilar kawo su zuwa birnin Yamai ya gudana tare da taimakon ofishin jakadancin Nijar dake birnin Trabulus cewa da Tripoli na kasar Libiya, tare da hadin gwiwar kungiyar kula da ’yan gudun hijira da kuma bakin haure ta MDD cewa da OIM.

Daga cikin wadannan ’yan Nijar da suka fito daga Libiya, yawancinsu sun wahala da shan azaba a kasar ta Libiya kafin ofishin jakadancin kasar Nijar dake birnin Tripoli ya dauki nauyinsu da ba su kulawa ta musamman kafin zuwansu a kasar Nijar.

Yawancin wadannan bakin haure ’yan Nijar matasa ne masu mabambantan shekaru da suka fito daga yankunan Tahoua, Zinder da Maradi, akasari da suka je kasar Libiya da zummar neman kudi ko bida, amma suka fuskanci matsalolin zaman rayuwa a kasarta Libiya da kuma rashin takardun zama.

Hukumomin gwamnatin rikon kwarya na kasar Nijar tare da hadin kungiyoyin agaji na gida da na kasashen waje sun taimaka wajen ba da kulawa da tarbon wadannan ’yan Nijar da hannu biyu biyu tare da binciken lafiyarsu da kuma ba su masauki kafin a maida kowane daga cikinsu kauyensa ko kuma yankinsa. (Mamane Ada)