logo

HAUSA

MDD ta saki dalar Amurka miliyan 100 na ayyukan agajin gaggawa ga kasashe bakwai

2024-02-21 10:49:15 CMG Hausa

Majalisar Dinkin Duniya ta ce asusun ba da agajin gaggawa na MDD ko CERF a ranar Talata ya ware dalar Amurka miliyan 100 don karfafa ayyukan agaji a kasashe bakwai dake matukar fama da karancin kudade a fadin nahiyar Afirka da ta Amurka da kuma yankin Gabas ta Tsakiya.

A cewar ofishin kula da agajin jin kai na MDD wato OCHA, Jamhuriyar Demokradiyar Kongo (DRC), Sudan, da kasar Sham ne ke kan gaba, inda kowannensu ya samu dala miliyan 20. Wannan tallafin dai an ba da shi ne da nufin taimakawa wadanda ke fama da rikice-rikice a gabashin DRC, da al’ummomi da suka rasa matsugunansu a Sudan saboda rikici, da kuma agazawa mutanen kasar Sham da ke cikin tashin hankali.

Bugu da kari, kasar Chadi za ta samu dala miliyan 15 don taimakawa ’yan gudun hijira da sauran rukunonin mutane masu rauni. Sauran kudaden an ware su ne ga Nijar (dala miliyan 10), Lebanon (dala miliyan 9), da Honduras (dala miliyan 6) don tallafa wa bukatun jin kai. (Muhammed Yahaya)