logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya da kamfanonin sarrafa siminti sun amince da karin farashin siminti

2024-02-21 09:59:28 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya da masana’antun sarrafa siminti dake kasar sun amince da kayyadadden farashin siminti da za a rinka sayarwa jama’a wanda ya kama daga Naira dubu 7 zuwa 8 a kan buhu mai girma kilogram 50, farashin kuma ya danganta ne da nisan wuri.

Bangarorin biyu sun amince da wannan sabon farashi ne a birnin Abuja, a cikin wata yarjejeniyar da suka kulla yayin wani taro da ya hada da ministan ayyuka da takwararsa ta kasuwanci da masu masana’antu.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Taron na gaggawa da gwamnati ta gudanar da masu masana’antun dai ya biyo bayan yadda farashin siminti ya yi tashin gauron zabi a ’yan kwanakin nan a kasar, wanda ya haifar da korafe-korafe da dama daga al’ummar Najeriya.

Yayin taron dai, wakilan kamfanonin sun sanar cewa muddin gwamnati ba ta cika alkawuranta ba a kan jerin matsalolin da masana’antun ke fuskanta zai yi wahalar gaske farashin siminti ya sauko kasa sosai kamar yadda al’ummar kasar ke tsammani.

Matsalolin dai sun hadar da rashin kyawun tituna, tarin haraji da tsadar makamashi, rashin tabbas na farashin dala a kasuwar musaya da kuma ayyukan masu fasa-kauri.

A jawabinsa, ministan ayyukan ta tarayyar Najeriya, Dr. David Umahi ya bayyana damuwar gwamnatin tarayya ne a game da tsadar siminti a kasar, lamarin da ya bayyana cewa, muddin ba a shawo kan al’amarin ba, ajandar gwamnati ta gina kasa zai gamu da cikas.

A kan korafin masu masana’antun kuwa Dr. David Umahi ya ce, “Tuni ministar masana’antu, ciniki da saka jari ta kasar ta tattauna da hukumar kwastam a game da batun fasa-kaurin siminti a kan iyakokin kasa wanda ya haddasa karancin siminti a wasu sassan kasar.”

A karshen taron kuma, ministan ya bayar da shawara ga masu masana’antun sarrafa simintin kan bukatar cewa, “Gwamnati na shawartar masu masana’antun sarrafa siminti da su samar da matakan sanya ido domin tabbatar da ganin ana aiki da sabon farashin siminti da aka kayyade a wannan rana.” (Garba Abdullahi Bagwai)