logo

HAUSA

Wakilin Sin: Kuri’ar kin amincewar da Amurka ta jefa kan kudurin tsagaita wuta a Gaza ta rushe matsayar kwamitin sulhun MDD

2024-02-21 11:19:07 CMG Hausa

Kwamitin sulhu na MDD ya kada kuri’a game da daftarin kudurin tsagaita wuta a Gaza nan da nan, wanda kasar Aljeriya ta gabatar a madadin kasashen Larabawa, to sai kuma ba a zartas da kudurin ba sakamakon kuri’ar kin amincewar da Amurka ta jefa.

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya jefa kuri’ar amincewa da kudurin, kana ya ba da jawabi don bayyana matsayin bangaren Sin. Zhang Jun ya ce bangaren Sin ya yi bakin ciki sosai game da yadda Amurka ta ki amincewa da daftarin.

Daftarin kudurin da Aljeriya ta gabatar a madadin kasashen Larabawa, na bukatar tsagaita wuta a Gaza nan da nan, da saki dukkan mutanen da ake tsare da su, da shigar da kayayyakin jin kai, da kuma hana tilastawa jama’a canja matsuguni, wannan ba ma kawai bukata ce ta gaggawa game da yanayin da ake ciki a yanzu ba ne, har ma yana da alaka da samar da abubuwan bukatun jin kai, don haka ya kamata dukkan mambobin kwamitin sulhun su nuna goyon baya ga kudurin.

Sakamakon jefa kuri’un ya nuna cewa, kwamitin sulhun MDD ya cimma matsaya guda daya kan batun, amma Amurka ta rushe matsayar. Ya ce matakin na Amurka ya jefa Gaza cikin yanayi mai hadari.

A yayin jefa kuri'ar ta wannan karo, daftarin kudurin da Aljeriya ta gabatar ya samu kuri'un amincewa 13, ciki har da kuri’ar kasar Sin, yayin da Birtaniya ta janye jiki daga jefa kuri'a. (Safiyah Ma)