logo

HAUSA

Wasu Kasashen Na Shirin Debo Ruwan Dafa Kansu

2024-02-21 17:30:19 CMG Hausa

Wasu rahotanni na cewa, Amurka da Turai na shirye-shiryen takaita shigar da motocin Sin, matakin da masu fashin baki suka bayyana a matsayin gurguwar dabarar da za ta kai su ga yin dan da-na-sani. Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning ta shaidawa taron manema labarai kan wannan batu cewa, wannan matakin zai shafi ci gabansu na dogon lokaci. Amma masu iya magana na cewa, duk wanda ya kona rumbunsa ya san yadda toka ke kudi.

Alkaluma sun nuna cewa a bara, kasar Sin ta fitar da motoci miliyan 4.91 zuwa kasashen waje, wanda ya zama na daya a duniya a karon farko. Bayanan da kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta fitar a kwanan nan, sun nuna cewa, a watan Janairun bana, kasar Sin ta fitar da motoci dubu 443 zuwa kasashen waje, adadin da ya karu da kashi 47.4 cikin 100 kan na shekarar 2023 wanda ya ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri.

A sa'i daya kuma, Amurka na tunanin yin amfani da wasu hanyoyin da ba kudin haraji ba, wajen takaita shigo da motoci masu fasahar zamani na kasar Sin da sauran sassan dake da alaka da su. Kungiyar Tarayyar Turai kuma ta kaddamar da wani bincike kan motocin Sin masu amfani da wutar lantarki.

Bayanan da kasar Sin ta fitar game da fitar da motoci na nuna irin ci gaban da ake samu a masana'antar kere-kere ta kasar mai inganci da ma muhimmancin kirkire-kirkire. Masharhanta dai na cewa, ya kamata kasashe su yi la'akari da muradun wasu yayin da muke kare muradun kanmu, da inganta ci gaba tare yayin neman ci gaban kanmu, samar da yanayi na kasa da kasa, mai dogaro da kasuwa, da doka don hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, ita ce alkiblar hada kai. Amma idan har wadannan kasashe da ma ’yan kanzaginsu idonsu ya rufe su ka ci gaba da aiwatar da matakan da za su raunana ci gabansu, to a karshe duk abin da biyo kar su zargi kowa sai kansu. Wai kowa ya debo da zafi to bakinsa. (Ibrahim Yaya)