logo

HAUSA

Masar ta yi takaicin gaza tsallakewar kudurin tsagaita wuta a Gaza

2024-02-21 10:38:28 CMG Hausa

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar, ta bayyana takaicin kasar game da gaza cimma nasarar amincewa da kudurin tsagaita wuta a Gaza, bayan gabatar da kudurin a zauren kwamitin tsaron MDD, sakamakon kuri’ar kin amincewar da Amurka ta jefa.

Sanarwar ta ce faduwar kudurin, na nuni ga gazawar dokoki, da tsarin aikin hukumomin kasa da kasa da ake da su, musamman kwamitin tsaro, wanda aka dorawa alhakin kariya, da warware tashe tashen hankula da dakile yake-yake.

Kaza lika, sanarwar ta bayyana matukar adawar Masar da mara baya ga tsagi daya, ko nuna son kai a fannin shawo kan yake-yake, da tashe-tashen hankula a sassa daban daban na duniya. (Saminu Alhassan)