logo

HAUSA

Sin ta sha alwashin zama jigon samar da daidaito a duniya mai fama da tangal-tangal

2024-02-21 09:34:00 CMG Hausa

A wannan makon ne, aka kammala taron tsaron shekara-shekara na birnin Munich dake kasar Jamus. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, yana daga cikin mahalarta taron na kwanaki uku na wannan shekara.

Rahoton taron ya jaddada damuwar da ake ci gaba da nunawa kan ra’ayoyin wasu kasashe na ganin wasu sun yi hasara, wasu kuma sun yi nasara, yayin da ake samun karuwar tashe-tashen hankula a fannin siyasa da karuwar rashin tabbas na tattalin arziki.

A cewar rahoton, gwamnatoci da dama ba sa mai da hankali kan cikakkiyar fa’idar hadin gwiwar duniya, maimakon haka suna kara nuna damuwa cewa, suna samun moriya kasa da ta wasu. Kasar Sin ta ba da gudummawar rundunar wanzar da zaman lafiya mafi girma a duniya, kana kasa ta biyu mafi ba da gudummawar kudin karo-karo na MDD.

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na ci gaba da kiyaye manyan manufofinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko da yaushe a duniya mai fama da tashin hankali. A jawabin da ta gabatar yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa inda ta yi karin haske game da halartar taron da Wang Yi ya yi, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta bayyana cewa, kamata ya yi hadin gwiwa da samun nasara tare, su zama tushen manufofin dukkan kasashe wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa. Kasar Sin tana son hada kai da dukkan bangarori, don samun nasara tare, da kaucewa hasara da dama, da kara tabbatar da tabbas a duniya, da samar da makoma mai kyau ga daukacin bil-Adama. Bangaren kasar Sin ya yi imanin cewa, ra'ayin cin moriya da faduwar wani, da neman mayar da wasu saniyar ware, da yunkurin yin fito-na-fito na wani gungu ne ke haifar da ra’ayin "tabka hasara". kasashe da yawa sun fahimci cewa, tilas ne a kaucewa hasara.

Haka kuma, ya kamata mu yi aiki tare, mu yi la’akari da muradun wasu tare da kare muradun kanmu, da inganta ci gaban hadin gwiwa tare da neman ci gaban kanmu, ta yadda za mu samu nasara tare, kuma nasara shi ne burin da ya kamata mu bi tare.

Wang ya ce, idan har ana son cimma nasara tare, kamata ya yi kasashe su zabi hadin kai kan rarrabuwar kawuna, hadin gwiwa kan sabani da bude kofa ga juna. (Yahaya, Ibrahim, Sanusi Chen)