logo

HAUSA

Ya kamata kasashen yamma su ji shawarwarin kasar Sin maimakon “damuwa da asara”

2024-02-20 11:25:06 CMG Hausa

An rufe taron tsaro na Munich karo na 60 a ranar 18 ga wata. Bisa la’akari da habakar rikicin Ukraine da karuwar rikicin Falasdinu da Isra’ila, an bayyana damuwa sosai yayin gudanar da taron na wannan karo. Ministan wajen Sin Wang Yi ya jaddada a cikin jawabinsa cewa, Sin ta sha alwashin zama jigon samar da daidaito a duniya mai tangal-tangal, batun da ya samu karbuwa sosai daga bangarori daban daban.

Taron tsaro na Munich shi ne dandalin tattauna tsarin tsaro na kasa da kasa da ya kai babban matsayi, wanda ke bayyana ra’ayoyin kasashen yamma musamman ma Turai kan yanayin tsaro da ci gaban duniya. Rahoton tsaro na Munich na 2024 da aka fitar yayin gudanar da taron ya yi tsammanin cewa, saboda karuwar rikicin siyasa da kuma karuwar rashin tabbas a bangaren tattalin arziki, kasashen duniya da dama ba sa kula da moriyar da hadin gwiwar kasa da kasa ya kawo, maimakon haka, sun fi mai da hankali kan yin takara don samun wasu manyan riba. A ciki kuma, yawancin al’ummun kungiyar kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki wato G7 suna ganin cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, kasashensu ba za su kasance kasashe masu tsaro da arziki ba.

A cikin shekarun nan, duniya na cike da tangal-tangal, kuma Sin ta dade tana kiyaye moriyar kasashen duniya da kuma ba da shawarwarinta a jere. Saboda haka, a yayin taron tsaro na Munich da aka gudanar a shekarun baya bayan nan, ana maraba sosai da taron da kasar Sin ke gudanarwa.

A cikin jawabin da bangaren Sin ya fitar a bana, an bayyana wani abu ga kasa da kasa, wato Sin za ta zama jigon samar da daidaito a lokacin da ake inganta hadin gwiwa tsakanin manyan kasashen duniya, sannan za ta zama jigon samar da daidaito a lokacin da ake tinkarar batutuwa da dumi-dumi. Bugu da kari, za ta zama jigon samar da daidaito a lokacin da ake gudanar da harkokin kasa da kasa. Daga karshe dai, za ta zama jigon samar da daidaito wajen karfafa ci gaban duk duniya baki daya. (Safiyah Ma)