logo

HAUSA

’Yan sanda: ’Yan bindiga sun kashe jami’in jam’iyya mai mulkin Najeriya a jihar dake tsakiyar Najeriya

2024-02-20 10:19:38 CMG Hausa

Wasu gungun ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe kakakin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya a jihar Filato dake tsakiyar kasar a karshen makon da ya gabata, kamar yadda ’yan sandan yankin suka bayyana a ranar Litinin.

Kakakin rundunar ’yan sandan yankin, Alfred Alabo, a cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya fitar a ranar Litinin din ya ce, an kashe Sylavnus Namang, sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a Filato ne, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wurin shakatawa a yankin Pankshin a daren ranar Asabar.

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, wadanda adadinsu ya kai kusan bakwai, sun kutsa cikin wani wurin shakatawa dake kan titin Pankshin zuwa Jos, inda suka yi garkuwa da mai wurin, a cewar sanarwar.

’Yan sanda sun aike da tawaga zuwa wurin bayan da suka samu kiran gaggawa, inda suka dakile yunkurin garkuwar tare da yin musayar wuta da ’yan bindigan. Dukkanin wadanda ake zargin sun tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu, a cewar sanarwar. (Muhammed Yahaya)